Daga Yakubu Abubakar Gwagwarwa
Wata kungiya mai zaman kanta a Kano Mai suna One Family dake gudanar da aikin tallafi ga al’umma ta gudanar da aikin samar da Rijiya da kuma gyara wani masallaci a garin yan joma dake mazabar yankatsari a karamar hukumar Dawakin kudu ta jihar kano.
Yayin kaddamar da bude Rijiyar, Shugaban dake kula da aikin tallafi na kungiyar Isma’il Muhammad, yace sun gudanar da aikin Samar da Rijiyar a garin Yan doma Saboda kawar da matsalolin ruwan Sha da ake fuskanta a garin .

Yace Rijiyar zata taimaka matuka wajen magance matsalolin ruwan da al’ummar yankin suka dade suna fama da ita. Ya kara da cewa sun gudanar da aikin gyaran masallacin ne dake kusa da Rijiyar sakamakon yadda ya jima da bukatar gyara shi.

“Wannan kungiyar ta mu ta One Family mun jima Muna gudanar da irin wannan aikin na Samar da Rijiyoyi a garurun da suke bukatar ruwa da Kuma gyaran makabartu hade da bada tallafin likafani da kayan aikin makabartun duk a matsayin sadakatujjariya”. Inji Isma’il Muhammad
Yace kungiyar su ta One Family bata da alaka da wata Siyasa ko kadan, Kuma suna samun kudin da muke gudanar da aikin mu ne ta hanyar tara taro da sisi daga ‘ya’yan kungiyar.

” Muna bukatar al’ummar wannan gari na Yan doma da su mai da hankali wajen bada kulawa ta musamman ga wadannan aiyuka da muka gudanar a garin, wanda hakan ne zai sa su dade suna morar Aiyukan”. A cewar Isma’il Muhammad
Da yake jawabin godiya a madadin al’ummar garin Mai unguwar garin na yan doma Malam Yunusa Ali Yan joma ya alkawarin baida kula da Rijiyar da aka Gina musu domin su dade suna amfanar Rijiyar saboda sun jima suna bukatar Rijiyar karin Rijiya a garin amma basu samu ba sai wanann lokaci.

Ya kuma yabawa kungiyar One Family saboda wanann aiki da suka yi musu wanda yace ya taimaka musu sosai wajen magance musu matsalar ruwan sha da ibada a garin.
Shi ma anasa jawabin limamin garin na yan doma Malam Muhammad Sani bayan ya yabawa kungiyar ta One Family bisa aikin gyara musu masallaci da ta yi, yace masallacin an gina shi ne tun a shekara ta 1988 kuma tun a wancan lokacin ba a gyara masallacin ba kamar yadda akai masa yanzu.

Ya kuma yi alkawarin cigaba da yiwa kungiyar da ‘ya’yan kungiyar addu’o’in samun cigaba da gudanar da irin wannan aikin na alkhairi don amfanin al’umma.