Ba mu Siyawa dan Ganduje Motocin Kamfe ba – Hukumar Haraji ta Kano

Date:

Hukumar tara kuɗaɗen shiga ta Kano (KIRS), ta nesanta kanta daga zargin karkatar da kuɗaɗe don siyan motocin kamfen ga ɗan gwamnan Kano Injiniya Abba Ganduje.

 

Wannan na zuwa ne bayan da jam’iyar NNPP ta zargi Hukumar da karkatar da wasu kuɗaɗe da kuma siyawa ɗan takarar majalisar tarayya na Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa a jam’iyyar APC.

 

KIRS ta ce bata shiga duk wani kamfe na siyasa a jihar Kano, inda ta yi gargadin cewa suna daukar matakin shari’a don ƙwato musu mutuncin da ake ƙoƙarin ɓata musu.

Talla

 

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban sashen sadarwa na hukumar KIRS, Alh. Rabiu Saleh Rimingado a ranar Alhamis wadda kuma ya aikowa kadaura24 , ya sake tabbatar da alhakin da doka ta tanada na ma’aikatar kudaden shiga.

 

Da yake maida martani ga wata sanarwa da daya daga cikin jam’iyyun siyasar ta fitar, na zargin hannu KIRS, Rabi’u ya bayyana cewa hukumar ta al’ummar Kano ce da kuma ma’aikatan gwamnati wadda aka ba wa amanar kula da kudaden shiga.

 

Rabiu ya ce KIRS a matsayinta na hukumar da ba ta da alaka da wani mutum ko wasu jama’a, bata da masaniya akan wancan zargi da ake yi mata.

 

Ya bayyana cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakin shari’a kan duk wani mutum ko gungun mutane da suka dukufa wajen jawo lamarin siyasa mara ma’ana ko bata sunan hukumar.

 

Wannan na zuwa ne bayan da Jam’iyyar siyasa ta NNPP ta fitar da wata sanarwa ta kafar yada labarai tana zargin KIRS da karkatar da dukiyar al’umma wajen siyan motoci domin yakin neman zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...