Daga Ibrahim sani gama
Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya, IPMAN, a yau Alhamis ta ce kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC/Pipelines and Product Marketing Company, PPMC, na da isasshen man fetur a kasa.
IPMAN ta ce akwai jiragen ruwa sama da 20 cike da man fetur a kasa suna jira a sallame su a Legas.

Jami’in hulda da jama’a na IPMAN, PRO, Suleiman Yakubu ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ta wayar tarho a Abuja, yayin da yake ƙarin haske a kan matsalar karancin mai da dogayen layukan motoci a gidajen mai da ke Abuja.
Yakubu ya ce abin da ya jawo karancin man ambaliyar ruwa me da ya shafi gadar Lokoja wanda hakan ya hana manyan motoci wucewa zuwa wurare daban-daban.
Ya ce karancin man fetur din ba wai da gangan ba ne, ibtila’i ne ya haddasa shi, inda ya ce gwamnati na yin duk mai yiwuwa don ganin an shawo kan matsalar.
“Ambaliya ta ragu a yanzu kuma motocin suna wucewa sannu a hankali, muna bukatar mu yi haƙuri har sai abin ya daidaita wanda yawanci yakan ɗauki kwanaki kaɗan,” in ji shi.