Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Dagacin sharada Alh iliyasu mu’azu ya yabawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa lambar girmamawa ta CRF da ya baiwa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.
yace wannan lambar girma da shugaban kasa muhd buhari ya bawa sarkin kano tazo a lokacin da ya dace saboda yadda Sarkin ya Maida hankali wajen hidimtawa al’ummar sa.

Yace kyawawan halaye da hakurin Mai Martaba Sarkin Kano na daya daga cikin halayen da suke daga mar tabar sarkin kano Alh Aminu ado bayaro a idanun duniya.
Ya Kuma yi fatan Alkhairi ga sarkin Bichi Alh nasiru Ado Bayero bisa samun tasa lambar yabon ta CON daga shugaban kasa Muhd Buhari.

Idan za’a iya tunawa a makon daya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa wasu daga cikin yan Nigeria sama da 100 lambobin girmama na kasa da shugaban kasa yake bayarwa lokaci zuwa lokaci.