
Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci sakataren gwamnatin tarayya da ya ci gaba bitar ayyukan ministoci da aka fara ranar Litinin na zango na uku da kuma na hudu na shekara ta 2022, inda ya ce rahoton zai zama wani bangare na bayanan miƙa mulki na gwamnatinsa gabanin zuwan sabon shugaba.
Jaridar Dailuy Trust a Najeriya ta ruwaito cewa Buhari ya bayar da umurnin ne yayin rufe taron bitar ayyukan ministoci a jiya Talata na 2022, inda aka kuma rattaba hannun kan dokar shugaban kasa na ganin kyautatuwar aikin gwamnati da kuma hadin-kai.
Shugaba Buhari ya bukaci dukkanin ministoci da kuma sakatarorin dindindin da su tabbatar da cewa sun miƙa rahoton ayyukan ma’aikatunsu zuwa ga ofishin sakataren gwmanatin tarayya domin yin ɓita.
”Za a gabatar min da bitar ayyukan domin yin duɓiya,” in ji Buhari.
Ya gargadi ministocin da sakatarorin dindindin da kuma shugabannin ma’aikatu cewa kada su watsar da aikin gwamnati don tafiya yakin neman zabe, inda ya ce ba zai lamunci hakan ba.
Ya kuma shaidawa mahalarta taron ɓitar ayyukan na ministoci cewa duk da fara yakin neman zabe gabanin zabukan 2023, za a ci gaba da bai wa aikin gwamnati muhimmanci da ya kamata.