Saudiyya ta yanke wa wani Ba’amurke ɗaurin shekara 16 a gidan yari

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Ɗan wani mutumin kasar Amurka da aka tsare a Saudiyya ya shaida wa BBC cewa an yanke wa mahaifinsa hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekara 16 saboda sakonnin Tuwitar da ya wallafa da ke sukar gwamnatin kasar.

 

An kama Sa’ad Ibrahim Almadi wanda ke da shaidar zama dan kasashe biyu wato Saudiyan da kuma Amurka ne a watan Nuwambar bara a lokacin da yake kan hanyarsa daga Riyadh zuwa Florida don ganin iyalansa.

 

Kotun ta Saudiyyar da ta yanke wa Sa’ad Ibrahim Almadi hukuncin na tuhumar da neman tayar da zaune tsaye a Saudiyya, da kuma mara baya da samar da kudi ga ayyukan ta’addanci.

Talla

Ɗan na sa ya ce shaidar da aka gabatar ta kunshi sakonni na Tuwita har 14.

 

BBC ta gansu waɗanda suka kunshi suka rushe wasu tsoffin wurare a biranen Makka da Jidda, saboda damuwar da ake da ita cewa wuraren tsoffin wuraren da ke nuna cewa kasar matalauciya ce da kuma sakonni akan kisan da aka yi wa dan jaridar nan Jamal Kashoggi.

 

Tun da farko kotun ta so ta yankewa Mr Almadi hukuncin zaman gidan yari na shekara 42.

 

Makonni biyu da suka wuce ne aka yanke masa hukuncin shekara 16 a gidan yarin da kuma haramta masa tafiye tafiye na tsawon shekara 16.

 

Ɗan nasa da ke zaune a Amurka ya kasa samun damar magana da shi.

 

Ya kuma shaida wa BBC cewa ya soki gwamnatin Amurka kan rashin daukar mataki a kan batun mahaifin nasa.To sai dai kuma wata majiya daga ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce ba ta da wani aiki illa kare ‘yan kasarta da ke waje.

 

Kazalika ma’aikatar ta ce ta yi magana da manyan shugabannin Saudiyyar a kan batun Almadi, to amma dan nasa Ibrahim ya zargi jami’an Amurkan da nuna rashin damuwa da hakin da mahifinsa ke ciki.

 

Ya ce baya son mahaifinsa ya mutu a gidan yari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...