Ba mu da kudin motar komawa jami’o’in da muke aiki – Shugaban ASUU

Date:

Shugaban kungiyar malaman Jami’o’i ta Najeriya, Farfesa Emmanuel Osodoke, ya ce mambobin kungiyar za su fuskanci wahala wajen komawa jami’o’insu a ranar Litinin saboda basu da kudin mota.

 

Shugaban na ASUU ya bayyana haka ne a jiya Lahadi, yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels dangane da janye yajin aikin na ASUU a ckin wani shiri mai suna Sunday Politics.

Talla

Farfesa Osodoke ya ce a lokutan baya malaman Jami’a na zama a gidajen da aka tanada musu kusa da makaranta, amma a yanzu ba haka lamarin yake ba domin suna zaune ne nesa da Jami’oin da suke koyarwa saboda yawancinsu basa samar musu wuraren zama.

 

“A can baya, malami zai iya taka wa da kafa yaje makaranta saboda suna zaune a cikin gidaje da aka tanada musu, amma a yanzu lamarin ya sauya, inda suke tafiyan kilomitoci 20 zuwa 30 kafin isa makaranta. Ta ya ya za su iya biyan kudin mota zuwa aiki,” in ji Osodoke.

 

Ya ce za su fuskanci wahalhalu wajen biyan kudin motar komawa aiki domin koyar da dalibai sbaoda ba a biya su ba har na tsawon wata takwas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...