Buhari yasa limamin da ya boye kiristoci a Jos cikin wadanda za’a baiwa lamaba girma ta MON

Date:

Daga Maryam Abubakar Tukur

 

Sheikh Abdullahi Abubakar, malamin addinin Islama a jihar Plateau, yana ɗaya daga cikin mutane 437 da gwamnatin tarayya ta tantance domin basu lambar girma ta kasa.

An zabi Abubakar don karbar lambar yabo ta MON.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai bayar da lambobin girman a ranar 11 ga watan Oktoba, a fadar gwamnati dake Abuja.

An ce Abubakar ya ɓoye Kiristoci 262 a cikin masallacinsa lokacin wani rikici da ya ɓarke a a wasu kauyuka 10 a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta jihar Plateau a watan Yunin 2018.

Da ya ke magana kan lamarin, malamin ya bayyana hakan a matsayin “wasan sadaukar da rayuwarsa”.

“Ban taɓa fuskantar mummunan tashin hankali irin wannan ba a rayuwata. Mummunan lamarin na baya-bayan nan ba a taba ganin irinsa ba,” inji shi.

Matakin nasa ya samu yabo sosai a fadin duniya, kuma a shekarar 2019, an sanar da malamin a matsayin daya daga cikin wadanda suka samu kyautar ‘yancin addini ta duniya.

Haka kuma a cikin jerin sunayen da aka saka akwai Muktar Gulma, malami da aka ce ya dage da tsayawa kan dalibansa a wani hari da aka kai a Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC) da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi, inda bayan ƴan ta’addan sun sake shi, sai ya ce sai ba zai tafi ba sai da ɗalibansa.

An ce a karshe an sake shi tare da wasu daliban.

Gulma yana cikin jerin sunayen wadanda aka zaba domin samun lambar yabo na MON.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...