Wata yar shekaru 3 ta rasu bayan wani mai shekaru 49 ya yi mata fyade a kano

Date:

Daga Aisha Abubakar Mai agogo
Wani magidanci mai shekaru 49, mai suna Baba Idi, ya shiga hannun ‘yan sanda a Kano bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 3 fyade, Khadija Adamu, aka, Yasmin.
 An kama wanda ake zargin ne a ranar 29 ga watan Agustan 2022 biyo bayan karar da mahaifin mamaciyar ya kai wa ‘yan sanda.
 A wata hira da ya yi da SAHELIAN TIMES, kawun marigayiyar, Bilyamu Abubkar, ya bayyana cewa mahaifiyarta ta zo yi mata wanka, sai aka ga jini a al’aurar ta.
Talla
 “Lokacin da mahaifiyarta ta tambaya, Yasmin ta tabbatar da cewa Baba Idi ne yake yi mata wani abu, kuma ya yi mata barazanar cewa zai kashe ta idan ta gaya wa mahaifinta,” in ji shi.
 A baya dai baba idi ya taba shigar da marigayiyyar zuwa wani shagon gidansu yarinyar kuma ya yi mata fyade.
Talla
 Yanzu haka manema labarai sun mallaki rahoton likita wanda ya tabbatar da an yiwa Yasmin fyade.
 A cewar kawun, daga baya aka kai Yasmin hedikwatar ‘yan sanda domin tantance wanda ake zargin.
 Ya kara da cewa “Lokacin da ta gan shi, sai ta fashe da kuka, tana mai cewa ya yi alkawarin zai kashe ta kuma ya baiwa kuraye ita su cinyeta,” in ji shi.
 Khadija ta yi rashin lafiya bata jima ba bayan kwana uku ta mutu tana cewa “shi, wanda ake zargin, “zai kashe ni.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...