Ƴan bindiga sun harbe wani ɗan kasuwa sabon gari Kano

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba harbe wani Inyamiri ɗan kasuwa, mai suna Ifeanyi a unguwar Sabongari a Jihar Kano.

 

Jaridar Kadaura24 ta jiyo cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 8:45 na dare a daidai ginin rukunin kantina na Azubros a kan Titin France da ke Sabongari a cikin birnin Kano.

Talla

Shaidun gani da ido sun ce ƴan bindigar sun iso wajen ne, sannan su ka harbe shi, inda ya mutu nan-take, su kuma su ka tsere.

 

“Dama, kana gani ka san shi su ka zo kashewa. Shahararren mai sayar da batira ne a Sabongari ,” inji shaidun gani da ido.

 

DAILY NIGERIAN ba ta samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sanda ta Kano, Abdullahi Kiyawa ba a lokacin haɗa rahoton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...