Daga Abubakar Sadeeq Ahmad
Dan majalisar tarayya mai wakiltar Karamar hukumar Nasarawa Hon. Nasiru Ali Ahmad ya bayyana cewa wajibi ne duk wani mai kishin karamar hukumar Nasarawa da jihar kano baki daya ya zabi Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin gwamnan jihar kano karkashin tutar jam’iyyar APC.
Nasiru Ali Ahmad ya bayyana hakan ne lokacin da yake kaddamar da ginin wasu ajujuwa guda 8 cikin guda 40 a mazabar dan takarar gwamna ta Gawuna, a kokarin sa na inganta harkokin ilimi a karamar hukumar Nasarawa.
Yace ya zamar wa duk wani dan karamar hukumar Nasarawa mai son cigaba ya zabi Dr. Gawuna saboda yace yana da yakinin idan Nasiru Gawuna ya zama gwamnan kano to al’ummar Nasarawa sai sun fi kowa amfana.
” Nasiru Gawuna mutum ne da ya dade yana taimakon al’umma tun lokacin yana shugaban karamar hukumar Nasarawa har ya zama kwamishinan harkokin noma Inda ya tallafawa kananan manoma da kayan noma na zamani, sannan kuma yazo ya zama mataimakin gwamna Inda suka yiwa jihar kano aiyukan cigaba masu tarin yawa”. Inji Nasiru Ali Ahmad
Dan majalisar tarayya na nasarawa yace Yan takarar jam’iyyar APC sun fi na kowacce jam’iyya chanchanta ,saboda gogewar da suke da ita da kuma iya mu’amala, kuma yace yana da yakinin idan Nasiru Gawuna da Murtala Sule Garo
Nasiru Ali Ahmad ya bukaci al’umma karamar hukumar Nasarawa da su zabi dukkanin yan takarar da jam’iyyar APC ta tsayar da su tun daga Dan majalisar jihar har zuwa dan takarar shugaban kasa, domin su cigaba da sharbar romon demokaradiyya.
