Daga Rahma umar kwaru
Yan sanda a Ogun sun kama wani dattijo mai shekaru 84, Stephen Jack, da laifin yi wa ƴar shekara takwas fyaɗe.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana haka a Abeokuta s yau Asabar, inda ya ce wanda ake zargin yana zaune ne a unguwar Okun Owa da ke Ijebu-Ode, kuma ya yi ƙaurin suna a neman ƙananan yara.

Ya ƙara da cewa mahaifin wanda aka kashen ne ya kai rahoton kubucewar Jack ga ‘yan sanda da ya lura cewa ‘yarsa na zubar da jini daga yankinta.
A kullum ana bukatar ruwa sama da Lita miliyan 200 a kano – Kwamishinan ruwa
Oyeyemi, Sufeto na ƴan sanda, ya bayyana cewa da aka yi masa tambayoyi, wacce a ka yi wa fyaɗen ta shaida wa mahaifinta cewa Jack ya yi lalata da ita.
2023: NNPP ta ƙaryata cewa ta ajiye Kwankwaso ta ɗau Tinubu a Osun
Ya kara da cewa an kai yarinyar zuwa babban asibitin Ijebu-Ode domin yi mata magani.
Kwamishinan ƴan sanda a jihar, Lanre Bankole, ya kuma bayar da umarnin a kai Jack sashen binciken manyan laifuka domin gudanar da bincike tare da gurfanar da shi gaban kuliya.