’Yan Kasar Lebanon Mazauna Kano Sun Samar Da Asibiti Na Zamani

Date:

Daga Rahama Umar kwaru

 

’Yan kasar kasar Lebanon mazauna Kano sun samar da wani asibiti na zamani a babban birnin jihar.

Hakan ta bayyana ne lokacin da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kai ziyarar gani da ido ranar Litinin a unguwar Bompai, a cewar Jami’in yada labarai na fadar, Balarabe Kofar Na’isa.

 

Asibitin na dauke da gadajen kwanciya 25, an kuma samar da na’urori na zamani domin gwaje-gwajen cututtuka, baya ga wurin kabar haihuwa, da kuma kula da jarirai.

Talla

Sarkin Kano ya yi murna da samar da asibiti , a matsayin wani babban cigaba da ya zo wa al’ummaar jihar kano baki daya.

 

Sannan ya ce, asibitin zai rage yawan fita waje da ’yan Najeriya ke yi domin neman magani.

Karanta‘Yan kasuwa a kano sun yabawa Ganduje bisa gyaran wasu titunan jihar

A jawabin shugaban asibitin, Abbas Hajaaj ga sarki a yayin ziyarar, ya ce sun samar da asibitin ne domin kishin jihar, an kuma sa masa suna asibitin ’yan Najeriya da ’yan Lebanon.

Murtala Sule Garo ya Sasanta Rikicin kungiyar APC Media Forum

 

A cewarsa, nan ba da dadewa ba za a yi bikin kaddamar da shi, bayan kammala daukar sabbin likitoci da ma’aikatan jiyya da na gudanarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...