Matasa sama da 300 sun sami tallafin Naira dubu goma – goma a karamar hukumar warawa

Date:

Ibrahim Aminu Riminkebe

 

Kimanin matasa maza da mata dari uku ne suka amfana da tallafin Naira dubu goma kowannesu daga majalisar kamar hukumar warawa domin su dogaro da kansu .

Kadaura24 ta rawaito Da yake mika tallafin kudaden shugaban karama hukumar ta warawa Alhaji Yusuf Andullahi Danlasan yace tallafin zai taimaka gaya wajen bunkasa tattalin arzki yankin.

 

Alhaji Yusuf Abdullahi inda ya bukace su wadanda suka ci gajiyar tallafin da suyi amfani da shi ta hanyar da dace domin su zamo masu dogaro da kansu.

Sarkin Kano ya je ta’aziyyar Sarauniyar Ingila Elizabeth II

Shugaban ya kuma jinjanawa gwamnati Dr Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda yake bunkasa rayuwa matasa da mata a kananan hukumomi 44 a fadin jahar nan.

Yayi amfanin da damar sa wajen jajintawa al’ummar karamar hukumar musamman ma mazar jigawa ,gishiri wiya da wasu yankuna bisa iftila”i na ambaliyar ruwa da ya mamaye ye gonakin su da gidajen su.

kungiyar cigaban unguwannin sarari, Mazugal da Arzai a kano ta yi gyaran makabartar wali mai Geza

Anasu jawabin daban-daban ,shugaban shuwagabanin Jam’iyyar APC Alhaji Bako Muhammad laraba da mai baiwa gwamna shawara akan bangaren gona Alhaji Ado Muhammad jemagu bukatar ‘ya’yan jam’iyyar APC sukai dasu cigaba da tallata jam’iyyar lunguna da sakuna domin takai ga nasara a zabe maizuwa.

Da yake gabatar da jawabin wakilin a majalisar dokoki na jahar mai wakilta karamar hukumar warawa, Alhaji Adinan Musa Danlasan ya godewa bisa hanken nesa Shugaban karamar hukumar na samar da tallafin kari ga matasa dari uku da suka fito daga mazabu goma sha biyar na karamar hukumar.

 

Malama Halima Ahmed da Hadiza Muhammad suna daga cikin wadanda suka amfana da tallafan kudaden sun bayyana farin cikin su, tare da yin alkawarin aiki dasu ta hanyar data kamata.

 

Taro bayar da tallafin kudaden ya sami halartar maitamakin shugaban karamar hukumar ta warawa Alhaji Ibrahima Saidu, Shugaban jam’iyyar APC Alhaji Sabiu Jinjiri Gogel, Kansiloli zababbu na daddu da masu bada shawara, da kuma shugabar mata ta jamiyar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...