Daga Rahama Umar Kwaru
Mai Martaba Sarkin Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya je ta’aziyyar Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth II, a Ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Abuja da yammacin ranar litinin .
Cikin wata Sanarwar da sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24 yace Sarkin yace domin nuna alhininsa ga gwamnati da al’ummar kasar Ingila dama duniya baki daya bisa rasuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth II.
Sanarwar tace lokacin da Alhaji Aminu Bayero yake Sanya hannu a littafin ta’aziyya, ya bayyana Sarauniyar a matsayin wadda ta sadaukar da rayuwarta wajen cigaban Zaman lafiya a duniya baki daya.
Kotu a kano ta wanke wani da ake zargi da kisan kai
Ya kuma yi fatan Sabon Sarkin daya gajeta zai dora kan abubuwan alkhairi da take gudanar wa tsahon Shekaru 70 da ta yi tana rike da sarautar Ingila.
Ida za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Sarauniyar Ingila Elizabeth II ta mutu a ranar Asabar data gabata, wanda yake ya sa mutane da dama cikin alhinin rashin ta a ko’ina a duniya.
