Daga Auwal Alhassan Kademi
Aminu Waziri Tambuwal, Gwamnan jihar Sokoto ya musanta cewa ya sauka daga mukaminsa na shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP.
Tambuwal dai yayi takarar shugaban kasa a PDP kafin ya janye wa Atiku Abubakar a zaɓen fidda-gwani na jam’iyyar.
Ya ƙaryata rahoton wata sanarwar da Darakta-Janar na ƙungiyar, CID Maduabum ya fitar a yau Juma’a.
“Ina mai sanar da jama’a da masu ruwa da tsaki a PDP cewa shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP (PDP-GF), Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal. Sabanin rahotannin kafafen yada labarai, Aminu Waziri Tambuwal bai ajiye mukaminsa na shugaban kungiyar ba.
“Mambobin kungiyar Gwamnonin PDP suna aiki a bayan fage don warware duk wata takaddama da ta shafi jam’iyyar. Za a gudanar da taron ƙungiyar nan ba da jimawa ba,” in ji shi.