Lalacewar titin Audu Bako barazana ce ga kasuwanci a kano – wani dan kasuwa

Date:

Daga Ibrahim Sani gama
Al’ummar dake gudanar da harkokin kasuwancin su akan titin Audu Bako da kewaye sun koka matukar ymda yadda titin ya jima da lalacewa amma gwamnati har yanzu bata gyara shi ba.
Ya kamata gwamnatin ta hannun  hukumar dake kula da gyara gyaren hanyoyi ta jihar kano (KARMA) ta kaiwa  titin da tashi daga railway zuwa roundabout din AA Rano zuwa titin Audu Bako way, daukin gaggawa, duba da yadda al’umma suke samun cokoson ababen hawa a lokuta daban daban, musamman masu gudanar da kasuwancinsu a yankunan.
Shugaban kungiyar matasan kasuwar masu magunguna kuma, mai rajin ci gaban alummar jihar Kano, Alh mamuda Zangon Kabo Wanda yayi magana a madadin al’ummar yankin yayi kiran ne a zantawarsa da wakilin Kadaura24.
Ya ce kamata yayi wanda alhakin gyaran ya rataya akansu suyi duba na tsanaki domin sanin gyaran da za a yiwa wadannan hanyoyi domin lalacewar ta yi mutukar ta’azzara.
” Lalacewar Wannan hanya ta sanya harkokin kasuwancin mu sun shiga wani hali, saboda mafi yawa na masu bin hanyar sun daina sakamakon lalacewar da hanyar ta yi”. Inji Zangon kabo
Yace rashin magudanan ruwa yana daya daga cikin abubuwan da suke haifar da yawan ambaliyar ruwa a yankunan da dama a fadin jihar kano, inda ya bukaci al’umma da su kasance suna aikin gayya da share magudanan ruwa domin kaucewa yawan ambaliyar Ruwa da ta yi yawa a halin yanzu.
Haka zalika, ya yabawa Gwamnatin jihar Kano, bisa kafa kwamatin da zai rika lura da gyaran magudanan Ruwa da guraren da suka yi gine gine ba bisa ka’ida ba, musamman a hanyoyin magudanan Ruwa, Wanda yin haka na daga cikin abubuwan dake haifar da Ambaliyar Ruwa da zubewar gine gine a lokuta daban daban.
Ya shawarci masu hannu da shuni da su ji gaba da tallafawa Matasa a unguwanni domin share magudanan Ruwa da yin ayyukan gayya don zai taimaka kwarai kaucewa yawan ambaliyar Ruwa.
Ko da wakilin Kadaura24 ya tuntubi Shugaban hukumar Karma wadda ita aka dorawa alhakin gyaran titunan da suka lalace a Kano, an ce masa yaje ya sami kwamishinan aiyukan na jihar Engr. Wada sale domin shi yake kula da hukumar tun da aka bashi mukamin kwamishinan, sai dai ya Gaza cewa komai akan lamarin.
Inda ya ki sauraron wakilin namu, Amma bamu Sani ba, rashin abun da zai fada ne Koko tsoron yan jarida yake , to Amma koma dai yaya ne ya kamata gwamnan al’ummar jihar kano da al’ummar jihar su Sani cewa wancan kwamishinan ya gaza sauke nauyin da aka dora masa domin ga matsala Amma ya kasa bayyana kokarin gwamnati wajen magance matsalolin da suka shafi rayuwar al’ummar jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Za mu kashe Sama da Naira miliyan 105. Dan Bunkasa Harkar ilimi a karamar hukumar Dala – Hon Surajo Imam

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Surajo...

Zaben 2027: Kwankwaso ya bugi kirji

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya...

Sha’aban Sharada ya sami sabon mukami

Daga Sharifiya Abubakar   Kungiyar ‘yan majalisun dake kula da tsaro...

Dan Majalisar NNPP ya fice daga jam’iyyar zuwa APC

  Yusuf Galambi dan majalisar wakilai ya sauya sheka daga...