Sabon kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar kano Alhaji Ibrahim Dan azumi Gwarzo ya yi kira ga daukacin alumar jahar dasu guji cushe magudanan ruwa, dan kauceawa yawaitar ambaliyar ruwa a jihar kano.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a zantawarsa da wakilin Kadaura24 a jihar kano.
Talla
Kwamishinan yace gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi ganduje na iya kokarinta wajen samar da aiyukan cigaba ga al’umma.
” Ba dai-dai ba ne mutane su rika zubar da shara a magudanan ruwa, saboda yin hakan sabawa hankali sannan Kuma zai haifar da matsalolin da zasu cutar da al’umma Masu tarin yawa”. Inji Dan Azumi
Talla
sannan Dan azumi gwarzo ya jajantawa daukacin Yan kasuwar da iftilain ambaliyar ruwan ya shafa, da Kuma mika ta’aziya ga iyalan wadanda suka rasu a rushewar ginin nan mai hawa biyu na kasuwar yan waya dake Kan titin Beirut.