Daga Maryam Alhassan Muhd
Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Amince da nada babban Mai taimakawa gwamna akan Kafofin yada Labarai Abubakar Balarabe Kofar Na’isa a matsayin babban Sakataren yada labaran Masarautar kano.
Kadaura24 ta rawaito amincewar nadin na dauke ne Cikin wata wasikar da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar kano Alhaji Usman Alhaji
Wasikar ta ce Gwamnan ya amince da nadin Abubakar Kofar Na’isan ne saboda da kwarewarsa a sha’anin yada labarai da Kuma ilimin da yake da shi a fannin.
Ba mu da wata matsala da Malam Shekarau – Kwankwaso
Abubakar Balarabe Kofar Na’isa bayan wanann Sabon nadi na babban Sakataren yada labara na Masarautar kano zai Kuma cigaba da riƙe mukaminsa na babban Mai taimakawa gwamna akan radio da Talabijin.
Ganduje ya sake tura sunan mutum 1, bayan 8 din da ya turowa Majalisa domin nadasu kwamishinoni
Gwamna Ganduje ya taya Sabon Mai magana da yawun Masarautar kanon Abubakar Balarabe Kofar Naisa tare da fatan zai gudanar da aikinsa bisa kwarewa don kare kimar Masarautar da jihar kano baki daya