Shekarau na shirin ficewa daga NNPP

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

 

Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, zai bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP, bayan wasu manyan alƙawura da ake zargin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi masa.

 

Malam Shekarau, wanda ke wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP a hukumance a wata wasika da shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya karanta a zaman majalisar a ranar 29 ga watan Yuni.

Majiya Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa Shekarau ɗin na samun tikitin kujerar Sanata a Kano ta tsakiya, kawai sai ya sumame zuwa Legas a ranar 24 ga watan Yuni domin ganawa da ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi domin ya zama mataimakin takararsa.

Jaridar ta kuma jiyo cewa tattaunawar da jam’iyyar Labour da Shekarau ke yi ta sha ruwa bayan da shugabannin APC da PDP suka fara kokarin ganin tsohon gwamnan ya dawo cikin su.

 

Ganduje ya tura sunayen sabbin kwamishinoni ga Majalisar dokokin Kano domin tantancewa

Yayin da shugabannin NNPP suka samu labarin ficewar Malam Shekarau, sai tawagar mutum 3 da suka haɗa da ɗan takarar gwamnan jihar na NNPP, Abba Kabir Yusuf, ɗan takarar kujerar Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila da kuma ɗan takarar majalisar wakilai, Kabiru Rurum, suka nemi ganawa da shi a daren Juma’a a Abuja, amma Malam Shekarau ya ƙi ganinsu.

Ana sa ran a yau Talata da ƙarfe 4 na yamma Shekarau zai kammala shirin ficewa daga NNPP zuwa PDP don morar tayin da Atiku Abubakar yayi masa.

 

Masana da bayyana babban kuskuren da Shekarau zai yi shine ya fice daga NNPP zuwa PDP, hakan zai nuna rashin nagartar siyasarsa da mutane suka dade suna faɗa.

Kwamitin shura a ganawar sa ta ranar Lahadi da ya gabata s gidan Shekarau

 

Majiya mai tushe da ke da masaniya kan wannan shiri na sirri da Shekarau ke yi da kuma ganawar daban da dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar; abokin takararsa Ifeanyi Okowa da; Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyochia Ayu, ta tabbatar da cewa tuni tsohon gwamnan ya “cimma yarjejeniya” da PDP kuma ana sa ran nan ba da daɗewa ba zai bayyana ficewar sa a hukumance.

A cewar majiyar, a ranar Lahadin da ta gabata ma, Shekarau ɗin ya kira taron gaggawa na majalisar shura kan harkokin siyasa, tare da sanar da ƴan majalisar halin da ake ciki.

DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa wani kwamiti mai mambobi 21 zai yi zaman gana wa a yau Talata da karfe 4 na yamma domin kammala shirye-shiryen sauya sheƙar da kuma hanyoyin da za a bi wajen magance suka da tofin alla-tsine da magoya baya da ma sauran jama’ar ga ri za su iya yi idan Malam Shekarau ya ɗauki wannan matakin na ba-zata.

Wata majiya da ke da masaniya kan taron ta ce, a wani ɓangare na shirin ficewar, dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar zai zo gidan Shekarau a Mundubawa domin neman dawo wa PDP kafin a fitar da sanarwar ficewar ta sa.

“Gaskiyar magana ita ce Atiku ya yi wa Mallam alƙawura masu gwaɓi kamar na minista da na ma’aikata. Ya kuma yi masa alƙawarin da nada shi a matsayin jagoran yaƙin neman zabensa a yankin Arewa-maso-Yamma da kuma kula da kuɗaɗen yakin neman zabe a yankin,” in ji majiyar.

Sai dai wata majiya ta kusa da Malam Shekarau ta ce Sanatan ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar NNPP ne ya kuma ajiye takararsa ta Sanata saboda jam’iyyar ta kasa baiwa yaransa takara.

“Shekarau bai ki daɗin yadda NNPP ta ƙi baiwa yaransa takara ba sai shi kaɗai kawai da ta baiwa takarar sanata. Kaga sai su ga kamar kawai kansa ya ke yinwa yaƙi ba su ba,”

DAILY NIGERIAN ba ta samu jin ta bakin kakakin Shekarau, Sule Yau Sule ba lokacin da ta yi ƙoƙarin tuntuɓar sa a kan wannan lamari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...