Daga Zara Jamil Isa
Hukumomi a Saudiyya sun yi bikin wanke Ka’abah bayan kammala aikin Hajjin bana.
Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman tare da shugaban masallatan Harami Sheikh Abdul Rahman da kuma Limaman Masallatan Haramin ne suka jagorancin wankin Dakin Allah.
Shekarau na shirin ficewa daga NNPP
Shafin intanet na Haramain, wanda ya wallafa hotunan wankin Ka’abah, ya ce an gudanar da shi ne a yau Talata.
Ana amfani ruwan zam-zam da turaruka masu kamshi, ciki har da miski da kuma tawul mai tsabta wajen wanke dakin Ka’abah.
Shekarau ya magantu kan batun ficewarsa daga NNPP zuwa PDP
Akan tanadi dukkan abubuwan da ake bukata kwana guda kafin a wanke dakin.
Haka kuma ana shafe sa’oi biyu wajen wanke dakin.
Wanke dakin Ka’abah ya faru ne tun daga lokacin Annabi Muhammad (SAW).