Ƴan Sanda sun kama matashin da ya tsaya kan kabari yana ta surfa ashariya a Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Rundunar Yan sanda a Jihar Kano ta Kama matashin nan da ya raba kafa akan kabarin wata mata yana surfawa wata dattijuwa zagi sabida sunyi fada da Yar data Haifa Kuma Yana dauka a bidiyo.

A yau Lahadi ne a ka tashi da ganin wani faifan bidiyo a kafafen sadarwa na wani matashi da ya raba ƙafa s kan wani labari ya an ta surfa ashariya a waya, ya na kuma dauka a bidiyo.

Sai dai kuma tuni Abdullahi Ƴar-dubu ya shiga hannun ƴan sandan Caji-ofis ɗin Sharada, inda yanzu haka an tusa keyar sa zuwa shalkwatar ƴan sanda da ke Bompai.

Kakakin rundunar ƴan sanda ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da kama matashin, inda ya ce, tuni Mukaddashin Kwamishinan Ƴan Sanda, DCP Abubakar Zubairu ya bawa DPO na Sharada, SP Abdulrahim Adamu umarnin a kamo wannan matashi.

Ya ƙara da cewa yanzu haka an kamoshi kuma an mikashi babbar shelkwatar rundunar yan sanda da ke bompai.

SP Kiyawa ya ce nan gaba kaɗan za a sanar wa da al’umma halin da a ke ciki.

Tuni dai al’umma su ka fara shi wa rundunar ƴan sandan albarka bisa tashi tsaye da ya ta kamo wannan matashin cikin ƙanƙanin lokaci, inda kuma su ka riƙa yi masa tofin alla-tsine.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...