Daga Isa Ahmad Getso
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ce ta kashe wani ƙasurgumi kuma jagoran ‘yan fashin daji da ke ayyukansa a Jihar Kaduna mai suna Alhaji Shanono tare da yaransa 17.
Kakakin sojan sama Edward Gabkwet ya ce Babban Hafsan Sojan Sama na Najeriya Air Marshal Oladayo Amao ya je Kaduna a ranar Laraba don duba ayyukan da rundunare ke yi a yaƙi da ‘yan bindiga a arewa maso yamma.
Kuma yayin wannan ziyarar aiki ce kwamandojin rundunoni daban-daban suka bayyana masa nasarar da suke samu.
“Ba zai yiwu mu ajiye makamanmu ba,” kamar yadda Oladayo Amao ya shaida wa kwamandojin.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce: “Bayan bayanan sirri da muka samu ranar 9 ga watan Agusta cewa Alhaji Shanono ya shirya ganawa da mayaƙnsa a ƙauyen Ukambo, rundunar Operation Whirl Punch ta aika jirgi zuwa wurin.
“Daga sama, an hangi ‘yan ta’adda a ƙarƙashin bishiyoyi da ke kan tudu kuma bayan tabbatar da cewa babu gidajen farar hula a wurin, sai aka bai wa dakaru damar kai hari.
“Rahotannin da mazauna yankin suka bayar sun ce an lalata bindiga fiye da 30 da kuma baburan ‘yan bindiga 20, yayin da aka kashe ‘yan fashi kusan 18, ciki har da Alhaji Shanono, sannan wasu suka raunuka.
“Majiyoyi sun kuma ce an ceto mutum aƙalla 26 da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su sakamakon hare-haren.”