Daga Rukayya Abdullahi Maida
Dan takarar Majalisar wakilai a kananan Kura Madobi Garun Malam a tutar jam’iyyar APC Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce addu’o’in da malamai da kuma kokarin da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ke yi ta fuskar tsaro sune suke sawa ake samun saukin matsalolin tsaro a jihar.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci garin garun babba dake yankin karamar hukumar garun malam don jajantawa al’ummar garin bisa yunkurin sace dagaci garin da wasu Yan ta’adda sukai a ranar talatar makon nan.
Yace Malam a jihar kano suna bada gagarumar gudunmawa wajen samun Zaman lafiya Saboda yadda a koda yaushe suke dugufa wajin yin addu’o’i tare da rokon Allah Madaukakin sarki ya kawo wa jihar nan Zaman lafiya da kasa baki daya.

” Mai girma gwamna na Sani baya wasa da duk wani lamari da ya shafi tsaro, saboda Yana sane da cewa sai da Zaman lafiya ne ake samun cigaba a gwamnatance da Kuma cikin al’umma baki daya, shi yasa kullum ya ke baiwa Hukumomin tsaro hadin kai tare da samar musu da kayan aiki na zamani domin dakile duk wani mummunan aikin a Kano”. Inji Musa Iliyasu
Ya yabawa al’ummar garin musumman Yan vigilante Saboda kokarin da sukai na ganin ba’a tafi da Dagachin nasu ba, Inda yace Wannan Abu da suka yi abun a yaba ne saboda sun nuna jarumta.
” Lokacin da na samu labarin Wannan lamarin nan take na kirawo Mai girma gwamna ta wayar salula don sanar da shi , Kuma ya damu matuka da ya ji labarin har yace inyi maka jaje tare da addu’ar Allah Madaukakin sarki ya kare afkuwar hakan a nan gaba”. Inji Kwankwaso.
Yadda Sojoji suka kashe kasurgumin Mai garkuwa da mutane da yaransa 17 a kaduna
Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi fatan Allah ya kara kare faruwar hakan a nan gaba, ba ma ga dagacin ba har ma da sauran al’umma nan gaba.
Idan ba’a manta ba a ranar talatar data gabata wasu yan ta’adda sun yi yunkurin sace dagaci garin garun Babba , idan daga bisani Yan vigilante da sauran Hukumomin tsaro suka hana tafiya da shi Kuma suka kwato shi.