Wani Dan kishain kasa kuma Shugaban kungiyar wadanda suka damu da halin da arewa take ciki Alhaji Rufa’i Mukhtar Dan maje yace matasa da dama a kasar nan suna cikin Mawuyacin hali sakamakon Rashin aikin yi da suke fama da shi.
Talla
Alhaji Rufa’i mukhtar Dan maje ya bayyana hakan ne a yayin wata zantawa da yayi da wakilin Kadaura24 a Gidansa dake Kano.
Ya kara da cewa rashi samun makomar matasa a kasar nan tana da nasa ba da Rashi samun jagoranci na gari domin da a kwai shugabanci na gari da tuni mafiya yawan masatan najeriya sun sami makoma mai dorewa .
Dan maje ya kara da cewa ,dole sai matasa sun san kansu sannan zasu San me ya kamata su yi, domin yawanci abinda yake faruwa na ta’addanci a a rewacin najeriya nada nasaba da rashin aikin yi.
” Matukar mahukunta basu jawo matasa a jikinsu ba to babu shakka al’umma ba zasu zauna lafiya ba, Saboda matasa su ne kashin bayan kowace al’umma, domin da su ne ake samun cigaba a kowane matakai”.
Ya kuma zargi yan Majalisun kasar nan da gaza tabuka komai akan duk wasu dokoki da suka shafi inganta Rayuwar matasan Nageria wanda yace hakan ya taimaka wajen kara tabarbara rayuwar matasa a kasar nan.