Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Kano ta sanar da rasuwar daya daga cikin Alhazanta na shekarar 2022, Sani Idris Mohammed a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
A sakon da sakataren zartarwa na hukumar alhazai ta jihar Kano Alh Muhammad Abbah Dambatta ya aikewa manema labarai, yace Sani Idris Mohammad dan karamar hukumar madobi ta jihar Kano ya rasu a ranar Juma’a a garin Makkah.

Alh Abbah Muhammad Dambatta ya ce an yi wa marigayiyar Sallar Janaiza a babban masallacin Harami kuma an yi jana’izarsa a makabartar dake kusa da masallacin harami na Shira da ke birnin Makkah.