Sanarwar Gaggawa…
Muna sanar da al’umma cewa Yan damfara sun kwace Shafin guda daga cikin wakilan kadaura24 wato Auwal Alhassan Kademi.
Shafin Mai sunan Auwal A Kademi sun kwace shi ne don a makon da ya gabata kuma mun fahimci ana turawa mutane sakon Neman su shiga wata harkar kasuwanci.
To Muna Sanar da jama’a cewa Auwal Alhassan Kademi bashi da ruwa akan duk abun dake faruwa a Shafin ,Kuma yana kira ga al’umma da su guji tura kudi ko aminta da duk wani sako da aka turo da Shafin mai suna AUWAL A KADEMI dake Shafin sadarwa na Facebook.
Muna godiya.