Gwamnatin Kano ta bayyana ranar Litinin a matsayin hutun sabuwar shekarar musulunci

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru
 Gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar Litinin, 1 ga watan Agusta, 2022 a matsayin ranar da hutu ga ma’aikata don murnar shigowaa sabuwar shekarar Musulunci ta 1445.
 Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba, ya taya daukacin al’ummar musulmin jihar murna Wannan  lokaci tare da bukaci kowa da ya yiwa kansa hisabi .
 Ya kuma yi kira gare su da su yi amfani da wannan lokaci wajen neman gafarar Allah, da kuma yin addu’ar Allah ya kawo was al’umma dauki ya kuma warware  matsalolin tsaro da suke addabi kasar nan da sauran matsaloli da dama.
 Gwamnan ya tabbatar wa al’ummar jihar kano cewa a shirye gwamnatinsa ta ke ta ci gaba da cika alkawarin da ta dauka na inganta rayuwarsu ta hanyar aiwatar da shirye-shirye da ayyuka da suka shafi jama’a.
 Sanarwar ta kuma bukaci wadanda har yanzu ba su karbi katin zaben su ba da su hanzarta zuwa su karba domin samun damar yin amfani da katin zabe a babban zabe mai zuwa wajen kada Kuri’a.
 Ranar asabar Mai zuwa ita ce ranar 1 ga watan al-muharram na sabuwar shekarar Musulunci, wanda kuma yayi dai-dai da  30 ga Yuli, 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...