Zan Murkushe Yan ta’addan kasar nan babu sassauci – Buhari

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara nanata aniyar gwamnatinsa na kawo karshen matsalar tsaron da kasar ke fuskanta, yana mai cewa ko kadan bai zai raga wa ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan da ke kai hare-hare a fadin kasar.

A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Lahadi, ya ce manyan hafsoshin tsaron kasar na iya bakin kokarinsu wajen ganin an kawo karshen matsalar ‘yan bindiga a kasar.

Ganduje ya bada tallafin Naira Miliyan 4 ga iyalan mamata 19 da suka rasu a hadarin mota daga Zaria zuwa Kano

Ya kuma jajanta wa tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Adamu Muazu, saboda kashe dan uwansa da ‘yan bindiga suka yi tare kuma da kame ‘yar uwarsa.

Yayin da yake bayyana ‘yan bindigar a matsayin makiya al’uma, Shugaba Buhari ya ce ya kadu matuka da wannan kisan.

Yajin aikin ASUU: Gwamnatin tarayya ta roƙi NLC da ta janye zanga-zangar da ta ke shirin yi

Ya kara da cewa ”Na yi matukar kaduwa da jijn labarin kashe dan uwanka, tare da kama ‘yar uwarka. Wannan masifa kullum karuwa take yi a kasar nan. Na sani kuna cikin halin damuwa, ina taya ku bakin-ciki”

”Matsalar tsaro ita ce babban abin da na sa a gaba, na kuma umarci manyan hafsoshin tsaron kasar da su yi iya bakin kokarinsu, domin kawo karshen wannan matsala da kasarmu ke ciki”. In ji Buhari

Wadannan kalaman na zuwa ne bayan ‘yan bindigar da suka sace gomman fasinjojin jirgin kasan nan na Abuja zuwa Kaduna, tun ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata, sun sake fitar da wani sabon hoton bidiyo da ke nuna mutanen da ake garkuwa da su cikin mummunan yanayi.

Kadaura24 ta rawaito a cikin bidiyon mai tsawon kusan minti goma sha daya, an ga ‘yan bindigar na lakada wa fasinjojin maza dukan tsiya da ita ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...