KEDCO ta bayyana dalilin da yasa ba a sami wutar lantarki ba a Kano yau asabar

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kamfanin sayar da wutar lantarki a Najeriya na Kano Electricity Distribution Company (KEDCO) ya sanar da kwastomominsa cewa za su kasance cikin duhu na tsawon awa takwas a ranar Asabar sakamakon gyaran da yake yi a wata tasharsa da ke jihar Kano.

 

Kamfanin na KEDCO dai shi ne ke bai wa jihohin Kano da Katsina da Jigawa lantarki, duka a arewacin Najeriya.

 

A cewar sanarwar da ya aike wa abokan hulɗar tasa, an ɗauki matakin ne saboda aikin gyara ɗaya daga cikin na’urorin rarraba wutar da ke Kumbotso a cikin birnin Kano.

 

Za a yi aikin ne daga ƙarfe 10:00 na safe zuwa 6:30 na yamma, a cewar KEDCO.

 

‘Yan Najeriya na fama da ɗaukewar wutar lantarki a dukkan sassan ƙasar a baya-bayan nan sakamakon lalacewa da babban layin lantarkin ke yawan yi.

 

Ranar Laraba ma sai da layin ya lalace da misalin ƙarfe 11:27 na rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...