Daga Aliyu Nasir Zangon Aya
Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Ahmed Idris, tsohon Akanta Janar na kasa tare da Olusegun Akindele, Mohammed Usman, da kamfanin Gezawa Commodity Market and Exchange Limited, a gaban mai shari’a Adeyemi Ajayi na babban kotun birnin tarayya dake zamanta a Maitama Abuja.
Kadaura24 ta rawaito Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ce ta gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume 14 da suka hada da satar Naira biliyan 109 da kuma cin amana.
EFFC tace bata Sami Rigar Mama ta Gwal Cikin kadarorin Diezani ba
Har ila yau, EFCC ta yi ikirarin cewa Ahmed Idris ya karbi kyautar kudi sama da Naira biliyan 15 daga hannun wani Olusegun Akindele tsakanin watan Fabrairu zuwa Disamba na shekarar da ta gabata, wanda Akindele ya mayar da kudin zuwa dalar Amurka, kuma kudin ba a bada dasu a kan ka’ida ba.
Dukkansu wadanda ake kara sun musanta tuhumar da ake yi musu.
Wani matashi dan Shekaru 25 ya rasu sakamakon fadawa kwata a Kano
Cif Chris Uche, lauyan su, ya roki kotun da ta bayar da belin su.
Mista Rotimi Jacobs, Lauyan masu gabatar da kara, ya nuna rashin amincewa da bukatar, yana mai cewa neman belin dole ne ya kasance a rubuce.
Bayan sauraron hujjojin nasu, Mai shari’a Ajayi ya bayar da umarnin tsare Ahmed Idris da wasu mutane biyu a gidan yari na Kuje har sai an kammala neman belinsu.
An dage sauraron karar neman belinsu zuwa ranar Larabar wannan makon.