Sanya matasa cikin shugabanci shi ne zai kawo karshen matsalolin Nigeria – Abulbashar

Date:

Daga Abudulamid isah zungura

Wani matashi Dan kishin kasa mai suna Abulbashar Yakasai yace Sanya matasa cikin sha’anin mulki a dukkanin matakai shi ne zai kawo ƙarshe matsalolin da Kasar nan take fuskanta.

Abulbashar ya bayyana hakan ne yayin wata ganawarsa da wakilin Kadaura24 a Kano.

Yace ya kamata a rika sanya matasa a cikin tsarin kowa ne shugabanci musamman a matakin kasa jihar dama kananan hukumomi, domin suna da gudunmawar da zasu bayar kasancewar suna da jini a jika kuma kwakwaliwarsu tana aiki yadda ya kamata.

Zargin badakala: Kotu ta aike da Akanta janar Ahmad Idris da wasu mutum biyu gidan yari

Abulbashar yace mafi yawa daga cikin shugabannin wannan lokaci sun sami damar shiga Sha’anin shugabanci ne tun suna matasa, Amma su yanzu sun hana matasa damarsu.

” Ya kamata shuwagabani susani cewa a duk lokacin da aka yi watsi da matasa to babu shakka hakan zai jawo koma baya a cikin al’umma kasancewar matasa su ne kashin bayan kowace al’umma” Inji shi

Wani matashi dan Shekaru 25 ya rasu sakamakon fadawa kwata a Kano

Yace bai kamata al’ummar kasar nan su kara zabar duk wani shugaba a kowanne mataki da bazai iya yin aiki na tsahon awa 20 ba, in har bazai iya aikin wadannan awowi ba to kamata yayi yaje ya huta.

2023: INEC ta fitar da sunan Sadiq Wali a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyar PDP a Kano

Haka zalika matashin ya kara da cewa matsalar Nigeria ya bakomai ne ya jawota ba face kin baiwa matasa dama domin su gwada irin baiwarsu a zahirance. ba wai a bari yan siyasa su rika amfani da su ta hanyar da bata dace ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...