Daga Rahama Umar Kwaru
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya mayar da martani ga masu kiraye-kirayen shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Iyorchia Ayu da ya yi murabus.
Tun da aka zabi gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin Dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDp, mambobin jam’iyyar da ke goyon bayan gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike suke ta kiraye-kirayen Ayu ya yi murabus, kamar yadda rahoton Daily News24 ya nuna.
Zargin badakala: Kotu ta aike da Akanta janar Ahmad Idris da wasu mutum biyu gidan yari
Kiran murabus din nasa ya zo ne a lokacin da ake zargin Sanata Ayu da yin amfani da mukaminsa na shugaban Jam’iyyar na kasa wajen musgunawa irin su Fayose da Ortom da sauran su wadanda tun da farko suka ba Wike a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar.
Yajin aikin ASUU: Gwamnatin tarayya ta roƙi NLC da ta janye zanga-zangar da ta ke shirin yi
Da yake magana kan wannan batu, Atiku, wanda ya fito a shirin safe na gidan talabijin na Arise a ranar Juma’a, ya ce shugaban jam’iyyar zai sauka ne kai idan shi atikun ya zama shugaban Najeriya a zabe mai zuwa.
“Da zarar na ci zaben, Sanata Ayu zai sauka daga mulkinsa kai tsaye. Mun sha fama da batutuwa irin wannan a baya, ba wannan ne karon farko da PDP ke fama da irin wannan rikici ba”. inji Atiku
Wani matashi dan Shekaru 25 ya rasu sakamakon fadawa kwata a Kano
Atiku ya kara da cewa Ayu zai ci gaba da mulki har sai ya ci zabe, yana mai jaddada cewa a ko da yaushe ana samun daidaiton mukamai a jam’iyyar.
Ya ce idan Shugaban kasa ya fito daga Arewa kai tsaye za a mayar da mukamin shugaban Jam’iyyar na kasa zuwa Kudu.