Daga Zakaria Adam Jigirya
A ranar Juma’a ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana sunan Sadiq Aminu-Wali a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano.
Jam’iyyar PDP ta jihar ta rabu gida biyu, inda ko wanne bangare ya gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar wanda ya haifar da Mista Wali da Muhammad Sani-Abacha dan marigayi shugaban mulkin soja a matsayin ‘yan takarar gwamna.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bangaren Shehu Sagagi da ya gabatar da Mista Sani-Abacha a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar.
Daily Nigerian ta rawaito cewa ofishin INEC na Kano a yau Juma’a ya fitar da sunan Wali tare da abokin takararsa, Yusuf Dambatta a matsayin ‘yan takarar gwamna da mataimakinsa a zaben 2023 ba Muhammad Abacha ba.
Abba Kabir-Yusuf, wanda ke daga tutar jam’iyyar , NNPP, shi ma ya shiga jerin sunayen tare da abokin takararsa, Aminu Abdulsalam.
Haka shi ma ɗan takarar gwamna a jam’iyar PRP, Salihu Tanko Yakasai, sunansa ya fito.
Sannan Sheikh Ibrahim Khalil, ɗan takarar gwamna a jam’iyar ADC, yana cikin jerin sunayen.