Zargin kalaman ɓatanci: Abduljabbar ya nemi a canja masa alƙalin da ke yin shari’arsa

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusif

 

Malamin addinin musulunci a Kano, Sheikh Abduljabbar Kabara, ya roƙi babbar kotun shari’a ta Kano da ta mayar da shari’ar da ake yi masa kan zargin cin zarafi zuwa wani alkalin.

 

A tuna cewa tun a ranar 10 ga watan Agusta 25 da 20 ga Disamba, 2019 ne dai Gwamnatin jihar Kano na tuhumi Kabara da laifuffuka guda huɗu da suka danganci kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad, SAW.

 

A zaman shari’ar na yau Alhamis, lauyan da ke kare 2qmda a ke ƙara, Dalhatu Shehu-Usman bai je kotun ba.

 

Wanda ake karar ya shaidawa kotun cewa lauyan nasa bai zo kotu ba sabo da ya rubutawa Khadi na jihar Kano wasikar canja shari’ar da ake yi zuwa wata kotu.

 

“Ina son a mayar da shari’ar ga wani alkali wanda ba shi da alaka da bangarorin biyu a shari’ar,” in ji shi.

 

Tun da fari, alkalin kotun, Ibrahim Sarki Yola ya tambayi Abduljabbar dalilin da ya sa ya ke so a canja shari’ar zuwa wata kotun.

 

Daily Nigeria ta rawaito Sarki Yola ya shaidawa wanda ake ƙara da ya faɗa wa lauyansa da ya zo kotu a zama na gaba, inda ya ƙara fada masa cewa idan so ya ke yi a sauya masa lauya za a sauya masa.

 

Ya kuma dage zaman zuwa 28 ga Yuli domin ci gaba da sauraron kariya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...