Sojoji sun sake gano wata daga cikin yan matan chibok

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Dakarun soji na rundunar Hadin kai, da ke yaki da Boko Haram a Najeriya, sun tabbatar da sake gano wata ‘yar makarantar Chibok mai suna Ruth Bitrus, wacce ta kubuta daga hannun mayakan Boko Haram tare da danta.

 

Jaridar Daily Trust a ta ruwaito babban kwamandan dakarun rundunar, Manjor janar GC Musa na bayyana hakan ranar Laraba.

 

A lokacin da yake mika wasu magunguna da hukumar raya yankin arewa maso gabas ta bai wa sojojin da ke aiki a yankin.

 

Kwamandan ya ce ”Idan za ku iya tunawa makonni da suka gabata, mun kubutar da ‘yan matan Chibok biyu, to yanzu ma mun sake kubutar da wata guda daya”

 

A ‘yan kwanakin baya ne dai, dakarun suka kubutar da ‘yan mata biyu a karamar hukumar Gazuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...