Daga yanzu kamfanin NNPC ya koma hannun yan kasuwa – Inji Buhari

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin mai na kasar wanda aka sauya wa fasali, inda a yanzu kamfanin na NNPC ya koma wani kamfanin kasuwanci mai zaman kansa

 

An yi kaddamarwar ne a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar a Abuja babban birnin kasar ranar Talata.

APC ta sa ranar da Tinubu zai gabatar da Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa

Shugaba Buhari ya fara ne da gode wa mahartar taron, wanda ya kira shi da ”mai dimbin tarihi”.

 

A jawabin da ya gabatar a wurin taron, Shugaba Buhari ya ce an mayar da ikon gudanar da kamfanin ga ‘yan kasuwa ne, saboda inganta shi, don samar wa kasar makashin da take bukata.

Hajjin bana: Wata Mahajjaciyar Nigeria ta ɓata a Saudiya

Ya kuma kara da cewa ”daga yanzu kamfanin NNPC ya koma karkashin gudanarwar ‘yan kasuwa, zai kasance kamfani mai zaman kansa ta yadda zai yi gogayya da takwarorinsa a fadin duniya, domin ci gaba da bunkasa hannayen jari sama da miliyan 200 tare da habaka fannin makashi a fadin duniya”.

 

”A yanzu doka ta dora wa kamfanin alhakin tabbatar da samar wa Najeriya wadataccen makashin da take bukata domin samun habakar tattalin arzikin ta hanyar farfado da wasu fannonin da ke bukatar makashin,” in ji Shugaban na Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...