Daga Abdulmajid Habib Isa
Daya daga cikin mabiya darikar kwankwasiyya da jam’iyar NNPP a Karamar hukumar Rano Bilya Ahmad Rano ya ce zasu tabbatar da aiwatar da akidar darikar Kwankwasiyya a jam’iyar NNPP domin cigaban al’ummar Nigeria.
Bilya Ahmad Rurum ya bayyana hakan ne lokacin kaddamar da kungiyar dake rajin tabbatarwa da kuma aiwatar da akidun darikar Kwankwasiyya wato “Movement For The Actualization of Kwankwasiyya Ideology” (MAKI) a takaice wanda ya gudana a garin Rurum.
Ya ce akidar Kwankwasiyya shine tallafawa ‘ya’yan talakawa da cigaban al’umma da samar da ayyukan yi ga matasa da kuma tallafawa na Kasa.
Mutanen Osun sun zabi wanda suke so, kuma dole a girmama shi – Buhari
Bilya Rurum ya ce tafiyar MAKI kamar ta Kwankwasiyya za su mayar da hankali wajen tabbatar da tsaro da inganta kiwo lafiya da cigaban harkokin ilimi da raya karkara da cigaban birane.
“Duk da yake lokaci ne na damuna, mutane suna gonaki suna aiki, amma sunji cewa taro ne na cigaba, taro ne na kwankwasiyya kuma muna hakan ne domin tallafawa tafiyar jagoran mu, Kuma ubanmu Injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwanso shugaban kasar mu na gobe insha Allah”, inji Bilya Rurum.
PDP ta lashe zaben Gwamnan jihar Osun
Ya ce “Muna kyautata zaton matukar injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwanso ya yi nasara a zaben shugaban Kasa to kowa zai amfana a Nigeria da kasa Baki daya, saboda mutum ne da yake da manufar cigaban al’ummar sa, mutum ne da yake da burin cigaban yankin sa, mutum ne da yake da rajin cigaban kasar sa da ma Nahiyar Afrika baki daya”.
“Za muyi amfani da lafiyar mu da ilimin da sanayya da dukkan abin da muke da shi wajen tallafawa tafiyar injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwanso domin zama shugaban Kasa”, inji Bilya.
Ya ce zasu tabbatar da wayar da kan Mata da Matasa domin su san Yancin su, su amfani da ilimin da Allah ya basu da wayewar da suke da ita wajen zabar shugabanni na gari da zasu kawo cigaban al’ummarmu.
Ya ce MAKI tafiya ce wacce aka kaddamar a mazabar Kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure kuma zasu tabbatar da kafa rassanta a dukkan kananan hukumomin Kano 44 da kuma jihohin Nigeria 36 ga mi da Abuja.
Yayi kira ga Mata da Matasa da su tabbatar sun yi rajistar Katin Zabe domin shi zai basu damar zaben Shugabani da zasu kawo cigaban yankin su da kuma tabbatar da sun zabi Kwankwanso a zaben 2023 da ke tafe.
A jawabinsu daban-daban, Shugaban kungiyar na Karamar hukumar Kibiya Aminu Shehu Kibiya da aka fi sani da Mai Gidan Ruwa da Aminu Ibrahim Bunkure shugaban kungiyar ta a MAKI a Karamar hukumar Bunkure ya ce mutakar jam’iyar NNPP ta yi nasara a dukkanin matakai a zaben dake tafe jagororin da aka zaba zasu tabbatar kawo karshen hauhawar kayan masarufi da ya damu al’ummar Nigeria dama duniya baki daya.
Shugabannin sun yi fatan kungiyar da ma NNPP zasu zama masalaha ga matsalolin al’ummar Kano da Nigeria baki daya.