Za mu kashe Kusan Biliyan 1 da Rabi Don Gina Titin Kwanar Garin-ali zuwa Sumaila – Yahaya Garin-ali

Date:

Daga Sani Magaji Garko

 

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta kashe kusan naira miliyan dubu daya da rabi domin gina titi mai nisan kilomita 18 a karamar hukumar Garko.

Shugaban hukumar samar da Tituna a yankunan karkara ta jihar Kano (RAAMP) Yahaya Adamu Garin-ali ne ya bayyana hakan a wajen kaddamar da aikin titin wanda ya tashi daga kwanar Garin-ali zuwa Garin-ali zuwa Dal ya hade da karamar hukumar Sumaila.

Yahaya Garin-ali ya ce za’a kashe naira miliyan dubu 1 da miliyan 477 da dubu 229 domin gina titin, wanda za’a yi wa magudanan ruwa a gefe-da-gefe, da yin gada inda ta kama, wanda tuni aka bawa dan gwangilar wani kaso don farawa.

Ya ce aikin zai saukaka harkokin Noma da kasuwanci a manyan garuruwa Biyar {5} wadanda suka hadar da Sumaila da Dal da Gani da Gumo da kuma Bura a yankunan kananan hukumar Garko da kuma Sumailan.

Sama da Maniyata 940 ne a Kano zasu rasa aikin Hajjin bana

Yahaya Garin-ali ya cigaba da cewa idan aka kamala aikin zai zama babu wata hanya sama da ita a karamar hukumar ta Garko.

Daga nan ya roki al’ummar yankin da su kasance masu bawa dan kwangilar hadin kai da goyon baya domin cigaban yankin, ya na mai cewa ginin hanyar zai taimaka wajen samar da aikin yi da kuma bunkasa tattalin arzikin yakin.

Idan inda naje, duk mukamin da na samu burina naga aikin nan ya tabbata, duk dan Garin-ali burin sa ayi wannan aikin, nayi kusan shekaru sama da shida (6) ina bun wannan aiki sai yau gashi ya tabbata, saboda haka ina godiya ga Allah, Alhamdulillah Burina ya cika”, inji Garin-ali.

“Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin zababban gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam ce zata gudanar da aikin, Kuma an Bada aikin akan kudi naira miliyan dubu daya (1) da miliyan dari hudu da saba’in da bakwai da dubu dari biyu da ashirin da tara da kwabo ashirin da hudu ( 1,477,229,000.74), wannan shine Kashi na farko na aikin, sannan akwai Kashi na biyu na aikin wanda shi Kuma kilomita shida (6) ne, Kuma tsawon shekaru bakwai (7) ina bin wannan aiki sai yanzu ne Allah ya tabbatar da shi”, inji Yahaya.

A nasa bangaren daya daga cikin jagororin siyasa a yankin kuma sakataren jam’iyar APC na jihar Kano Ibrahim Zakari Sarina ya bukaci al’ummar yankin da su tabbatar sun yi rejistar katin zabe tare kuma da zabar jam’iyar APC a yankin domin dorewar ayyukan raya kasa.

Zakari Sarina ya kuma bukaci shugaban hukumar ta RAAMP da ya kara fadada ayyukan zuwa wasu mazabu na yankin da suka hadar da Makadi da Sarina da Gina gadar kusa da gidan tsohon shugaban Karamar hukumar Garko Alhaji Mansur Musa (Alhaji Mansur) da gadar Audiga da ma wasu da dama.

Akwai ayyuka da dama da suke damun mu a Garko, misali Gadar Audiga, gadar gidan Alhaji Mansur, su ma zababbun mu zama saka su a gaba, zamu hura musu wuta, zamu tabbatar mun hada kai munyi magana da murya daya domin tabbatar mun samar da masalaha ga matsalolin mu”, inji Sarina.

Ya ce “muna godiya ga Mai girma gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam da ya sahale Maka, kazo ka yi wannan aikin, Muna fatan al’ummar Garko da ma Kano zasu dunkule tare da zabar jam’iyar APC domin tabbatar da dorewar ayyukan cigaban al’ummarmu”.

A jawabinsa, shugaban karamar hukumar Garko Salisu Musa Sarina ya ce majalisar yankin zata Bada dukkan gudun mowar da ake bukata don samun nasarar kammala aikin akan lokaci.

Yayi fatan Dan kwangilar zai gudanar da aikin Mai inganci domin dadewa ana amfana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...