Daga Abdullahi Tukur
Al’ummar Masarautar Zuru da ke Jihar Kebbi sun koka kan matsalar tsaro da ke addabar su a kowanne lokaci a yanki.
Wani dattijo mai suna Garba Musa Maidoki, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Zuru, ya ce, lamarin ya Kawo koma baya a harkokin zamantakewa da tattalin arzikin al’ummar su musamman a fannin kasuwanci da noma.
Ya bayyana cewa, ana kisan jama’a, a kona yara, a ruba ruwan batur shigar a cikin al’aurar mata, kuma a kona hatsi a kauyuka, satar shanu da kuma sace-sacen mutane sun yawaita abun zasu iya kiransa da kisan kare dangi saboda basa samun taimako daga hukumomin tsaro a yankin.
“Muna cikin wani mawuyacin hali, mun kai rahoton halin da muke ciki ga gwamnatocin Jihohi da na tarayya amma abubuwa na ci gaba da tabarbarewa.” Inji Musa Maidoki
A cewarsa, an gudanar da taro a garin Zuru kimanin shekaru biyu da suka gabata tare da shugabannin hukumomin tsaro na kasa, gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu, Sarkin Zuru da dai sauran su wadanda suka halarci taron amma har zuwa yau lamarin bai chanza ba.
Maidoki ya yi nuni da cewa, sojoji da ‘yan sandan da aka tura domin tabbatar da tsaro a yankin ba su da isassun kayan aiki, wanda hakan ya sa suke janyo asarar rayuka da dama da ke haifar da fargaba da rashin tabbas a zukatan al’ummar Masarautar Zuru .
Ya kara da cewa, al’ummar Zuru ‘yan kasa ne masu bin doka da oda kamar yadda jami’an tsaro ke nunawa a duk fadin kasar nan ta hanyar sadaukar da rayuwarsu domin jin dadin rayuwar ‘yan Nijeriya baki daya.
Maidoki Al’ummar yankin za su ci gaba da tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa har sai an magance matsalolin tsaro a Masarautar Zuru.