Daga Rukayya Abdullahi Maida
Babbar kotun jiha Kano Mai lamba 17 dake zamanta a Milla road ta karbi shaidu guda 2, yayin gudanar da shari’ar Umar Idris farawa, wanda ake zargi da kisan Sabi’u Umar farawa tun a ranar 2 ga watan satunbar 2021.
Daya ke bada shaida mutum na farko Aminin mamacin Mai suna babangida mansur, ya bayyana cewa shi ya kama Wanda ake zargi bayan da ya cakawa mamacin wuka a wuya har kuma aka kaishi ga hukuma don gudanar da bincike.
Shaida na biyu Umar Abubakar ya shaidawa kotu cewa an cakawa mamacin wuka a wuyansa ne kamar yadda ya gani yayin da ake yi masa wanka gabanin ayi jana’izar sa.
Da yake yiwa manema labarai Karin haske Lauyan gwamnati dake kare masu Kara barista lamido Abba soron dinki, ya bayyana cewa sun gabatar da hujjjinsu Kuma sun bayyana abinda suka sani ga kotu don haka zasu Jira Adalcin kotu.
Sannan Kuma yace ana tuhumar Wanda ake zargin ne da satar lefen mamacin da farko kafin daga baya ya kashe shi ta hanyar caccaka masa wuka.
Anasa bangaren Lauyan dake kare Wanda ake zargi da kisan Kan, barista M M Bello ya bayyana cewa an dauki shaidu biyu, “sai dai a matsayin mu na lauyoyi munyi tambayoyi ga shaidun da Lauyan gwamnati ya gabatar don tabbatar da cewa shaidun sahihai ne ko kuwa akasin haka, kasancewar gaba ce guda biyu idan zargin gaskiya kotu zatayi hukunci, idan kuwa ba haka bane kotu ce zata tabbatar da Adalci a tsakani kan abinda ake Kai” a cewa barista muhd Bello Lauyan dake kare Wanda ake zargi.
Mai Sharia sunusi ma’aji ya daga sauraren shari’ar zuwa ranar 30 ga yuni don cigaba da Karbar shaida.