Daga Zara Jamil Isa
Hukumar zabe mai zaman kanta ta tabbatar da Bashir Machina a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Yobe ta Arewa.
Ingantaccen kwafin rahoton INEC daga zaben ranar 28 ga Mayu, 2022, ya nuna Machina ya samu kuri’u 289 cikin wakilai 300, wanda ke tabbatar da cewa shi ne ya lashe zaben fidda gwani kuma ya fito a bisa doka.
Takardar wadda ofishin zabe ya tabbatar a ranar 23 ga watan Yunin 2022, ba ta ambaci Ahmad Lawan ba, shugaban majalisar dattawan da ya yi ta kokarin kwacewa Machina kamar yadda shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Adamu yayi ikirari.
Abdullahi Adamu ya sanya sunan Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a zaben Sanatan Yobe ta Arewa da aka shirya gudanarwa a watan Fabrairun 2023, yana mai cewa an gudanar da zaben fidda gwani a asirce inda ake ce Ahmad Lawan ya yi nasara.
Ko da yake Bashir Machina ya samu shaidar lashe zaben, amma har yanzu yana sa ran za a kara gwabzawa lokacin da INEC za ta tsayar da ‘yan takarar da za su tsaya takara a jam’iyyun siyasa daban-daban a makonni masu zuwa. INEC ta ce ba ta da hurumin zabar dan takara a zabe, duk da cewa tana da hurumi na tabbatar da an gudanar da zabe.
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya fara yunkurin karbe tikitin ne daga hannun Machina bayan ya sha kaye a babban taron jam’iyyar da ke mulki, wanda Bola Tinubu ya samu nasara a ranar 8 ga watan Yuni.
