Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kwamishiniyar harkokin mata da cigaban al’umma ta jihar Kano Dr Zahra’u Mohd Umar ta bukaci al’ummar jihar nan dasu tabbatar sun mallaki katin zabe domin zabar shugabannin nagari.
Cikin sanarwar da jami’ar hulda da jami’a ta ma’aikatar mata Bahijja Malam kabara ta aikowa kadaura24, ta ce Dr. Zahra’u Umar ta yi wannan kiran ne a lokacin da ta karbi bakuncin kungiyar yada an gizon Gawuna,Garo, Tinubu,da arewa Mata zallah wadanda suka kai mata ziyarar ban girma a ofishinta.
Ta bayyana muhimmancin rajistar katin zabe Inda ta bukaci al’ummar jihar musamman mata da su karbi katinsu domin su samu damar yin amfani da katin zaben wajen zabar Wadanda zasu tallafawa rayuwar su.
Kwamishinan ta kuma jaddada bukatar wayar da kan jama’a yadda ya kamata da kuma wayar da kan jama’a a yankunan karkara domin samun katin zabe na dindindin ya zama makamin da za ayi amfani da shi wajen fafutukar kwato ‘yanci.
Ta yaba da kokarin kungiyoyi musamman shirya laccoci na yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi tare da fadakar da Fulanin Riga kan muhimmancin katin zabe na dindindin, karfafa mata da hada kan matasa.
Dokta Zahra’u ta kara da cewa, gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje da mai dakin sa a shirye suke a kodayaushe don tallafa wa duk wani yunkuri na inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.
Ta kuma bada tabbacin goyon bayan ma’aikatar domin cimma burin da ake so.
A nasu jawabansu na daban, wacce ta ya kafa kungiyar Arewa Mata zallah hajiya Hauwa Marke wacce ta wakilci shugabar kasa Hajiya Jamila Abdullahi da kuma shugaban kungiyar crown media Gawuna Garo and Tinubu, Malam usman tsakuwa ya yaba da karimcin da kwamishiniyar tayi musu tare da bada tabbacin amincewar su wajen ciyar da jihar Kano da Nigeria gaba.

