Daga Aminu Garba Indabawa
Shirin bunkasa noma da kiwo na jahar Kano (KSADP) yana kara bunkasa musamman ta fannin bunkasa abinci da tattalin arzikin manoma a jihar Kano da kasa baki daya.
Kadaura24 ta rawaito Daya daga cikin manoma ne a nan kano mai suna Malam Mukhtar Dahiru ne ya bayyana hakan a garin Laraban Gadon Sarki dake karamar hukumar Warawa a nan jahar Kano.
A lokacin da cibiyar Sasakawa Africa Association guda daga cikin wadanda suke gabatar da shirin na KSADP, a lokacin ta shirya wani gagarumin taron nunan amfanin gona a garin Tofai dake karamar hukumar Gabasawa da kuma garin Larabar Gadon Sarki dake karamar hukumar Warawa.
Malam Mukhtar ya tabbatar da cewar sun samu gagarumin cigaba ta fanni amfanin gona da sabbin dabarun zamani da shirin ya zo musu da su, inda ya jadda cewar babu shakka za su cigaba da amfani da wadannan dabaru da kuma sababbin irirrikan da ake zuwar musu da shi.
Taron ya samu halarta mataimakin shugaban cibiyar Sasakawa na kasa Dr. Abdulhamid Gambo da shugaban shirin KSADP a Sasakawa Comr. Abdurrashid Hamisu Kofar Mata, da iyayen kasa da sauran manoma.
A karshe an bukaci manoma da su cigaba da yin amfani da dabarun da suka samu a cikin shirin na KSADP.