An yi zaben fidda gwanin sanata da Ahmad Lawan a Yobe -Shugaban APC

Date:

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawan kasar Sanata Ahmad Lawan ya shiga zaben fitar da gwani na neman takarar kujerar Sanata a Yobe ta Arewa da jam’iyyar ta gudanar.

Jaridar The Nation ta ambato Sanata Adamu yana yin wannan kalami a lokacin da ya jagoranci wasu ‘yan jam’iyyar zuwa fadar Shugaba Muhammadu Buhari, domin gabatar da zababben gwamnan Jihar Ekiti Biodun Oyebanji.

Sai dai mutumin da ke ikirarin lashe zaben, Bashir Machina na ci gaba da bayyana cewa Sanata Ahmad Lawan bai shiga takarar Sanata a Yobe ba, ya shiga takarar shugaban kasa ne.

Rahotanni sun ce Machina ya yi barazanar maka jam’iyyarsa kotu, bayan da wasu bayanai ke cewa sunan Ahmed Lawan aka mika wa hukumar zabe ta INEC a matsayin wanda zai yi wa jam’iyyar APC takara daga Yobe ta Arewa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...