Daga Auwal Alhassan Kademi
Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bayyana bukatar ma’aurata su rika mutunta ka’idojin aure a kodayaushe domin samun nasara da jin dadin zaman auren.
Kadaura24 ta rawaito Aisha Buhari ta bayyana haka ne a wajen wata liyafar daurin aure na Iman Tanko Almakura, diyar Dakta Mairo Almakura, mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa kan harkokin zaman a Abuja.
Ta kuma bukaci ma’auratan da su yi riko da ka’idojin aure a gidajensu ta hanyar bin ka’idoji da girmama juna don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Uwar gidan shugaban kasar ta kuma bayar da shawarar cewa dole ne ma’aurata su rika zuwa neman shawarwarin da ya dace kafin aure domin a samu fahimtar juna a tsakanin su.
Duk mun san yadda aka yi tarbiyyar amaryar, na tabbata za ta zama mace ta gari mai kula da mijinta, ni ma zan so in ja hankalin maigidan, Sadiq Kaoje, don raya soyayyar da kuke yi. amarya.
“Na tabbata da zabi koyarwar littattafi mai tsarki na alqur’ani mai girma da hadisan annabj S A W za ku sami zaman lafiya a aurenku,” in ji ta.
Saboda haka, uwargidan shugaban kasar, ta umurci ma’auratan da su rika neman ilimin yadda annabi S A W a ya koyar da yadda ake zaman sure a kodayaushe don a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ma’aurata.
A nasa bangaren, gwamna Simon Lalong na jihar Filato, wanda ya yi magana a madadin kungiyar gwamnonin Najeriya, ya yi fatan ma’auratan zasu s zauna lafiya da juna don samun jin dadin zaman aure na har abada.


