Bayan matsa wa yan jarida da sauran mambobin APC su bar wurin, jami’an tsaron sun kuma harba barkonon tsohuwa, hakan ya tilas wa mutane guduwa neman mafaka.
Daily Trust ta rahoto cewa tun safe yan jarida ke dakon takardar shedar sahalewa su gudanar da aikin su na ɗakko labarai daga kwamitin midiya na taron karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Sule.
Tun mako biyu kafin zuwan wannan rana, gidan jaridu suka kammala shirye-shirye tare da ware ma’aikatan da zasu tura don aikin nemo labarai a wurin taron.