2023: Abubuwan da baku Sani ba kan zaben wanda zai yiwa APC takarar Shugaban kasa

Date:

A ranar Talatar nan ne jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta fitar da gwani da zai kasance ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Sai dai za ta shiga fagen zaɓen fitar da gwanin ne dai-dai lokacin da ta shiga ruɗani da rarrabuwar kai game da batun ɗan takarar masalaha da goyon bayan mafi rinjayen APC.

Buhari ya bayyana matsayarsa Kan wanda zai yiwa APC takarar Shugaban kasa

An kasa samun jituwa kan batun, abin da kuma ya yi matuƙar yamutsa hazo sa’o’i kafin babban taron na ranar Talata.

Ƙoƙarin haɗa kan tsintsiya, ya nemi wargaza ‘ya’yanta. APC dai ta gaza cimma masalaha wajen fitar da ɗan takara shugaban ƙasa na masalaha.

A jiya, an yi ta samun bayanai masu cin karo da juna game da wane ne mutumin da shugaban ƙasar ke so a mara wa baya.

Da dumi-dumi: Gwamnonin arewa sun yi fatali da Matakin tsayar da Ahmad Lawan

Gwamnonin jam’iyyar sun yi taro da Shugaba Muhammadu Buhari, inda shugaban gwamnonin arewa Mista Simon Lalong ya ce Buhari ya faɗa musu cewa ba shi da ɗan takara, amma su sun haƙiƙance cewa a cikin masu neman takara daga kudu ne ya kamata APC ta darje ɗan takarar shugaban ƙasa.

Sanarwar fadar shugaban ƙasa ta ƙara tabbatar da matsayin Buhari cewa ba shi da “ɗan gaban goshi,” kuma bai nuna wani “shafaffe da mai” ba.

Ya kuma sha alwashin cewa “ba za a ƙaƙaba wa APC wani ɗan takara ba.” Gwamnonin dai sun ce duk da ra’ayinsu ya saɓa da na shugaban ƙasa, amma masalahar Nijeriya suka duba kan matsayarsu, kamar yadda Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya ce su mutane suke dubawa, kuma ba lallai ya kasance abin da suke fada ya farantawa wasu rai ba.

”Mutum goma sha uku cikin sha hudu, mun fadi ra’ayinmu, amma ba um tilastawa kowa ba, mu dai mu na kiran wanda bai amince ba ya yadda, idan kuma ba haka ba shi kenan sai a hadu a fili. Amma ko da ka na da niyyar takara ka ji shugabanni na cewa ayi hakuri, a samu hadin kai, saboda mutane 23 ba za su taba zama ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ba, mutum guda ne kadai zai iya zama”.

Tuni da ɗaya daga cikin gwamnonin APCn, ya sa ƙafa ya shure wannan matsaya.

Gwamna Yahya Bello ya yi tsalle ya dire cewa sai an fafata da shi a filin neman takarar shugaban ƙasa na APC a yau.

Ana tsaka da wannan dambarwa kuma sai ga wata ƙurar ta turnuƙe. Bayanin da aka ambato shugaban APC Abdullahi Adamu na yi wa ‘yan kwamitin zartarwar jam’iyyar cewa Shugaban Majalisar Dattijan Nijeriya Ahmed Lawan ne ɗan takararsu na maslaha, ya janyo ta da jijiyoyin wuya.

Magoya bayan wasu masu neman takara sun cika da guna-guni da ɓacin rai, har ma suna nuna shakku kan tabbacin samun adalci daga shugaban na APC. Kamar yadda Mustapha Yunusa Mai Haja, jigo a tafiyar Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa BBC.

Cikin yanayi na rarrabuwar kai tsakanin shugabancin APC da gwamnonin jam’iyyar da kuma fadar shugaban ƙasa, alƙibla a yanzu dai ta karkata kan daliget.

Masu wuƙa da nama ke nan, kan mutumin da zai yi wa APC takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 cikin manema kimanin 20.

Abin da har yanzu nuna cewa takarar shugaban ƙasa a APC dai sai mai tsananin rabo.

Ga dukkan alamu dai wankin hula ya kai dare ga jam’iyyar mai mulkin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...