Delegates 2,340 ne ake sa ran zasu kada kuri’a a zaben fidda gwani na jam’iyar APC na dan takarar shugaban kasa da za a gudanar yau a filin wasa na Eagles Square dake Abuja.
‘Yan takarar 20 da uku ne zasu fafata a zaben da ake saran fidda mutum guda wanda zai yiwa jam’iyar ta APC takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.
Kadaura24 ta rawaito Manyan “yan takarar da ake ganin zasu fafata a zaben na yau sun hada da matemakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo da tsohon gwamnan jihar Lagos Bola Ahmad Tinubu da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad lawan da gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi da ministan sufuri Rotimi Amechi da kuma wasu mutum tara duk da cewar wasu daga cikin yan takarar sun janye.
A cewar shugaban jam’iyar ta APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu, ya ce tuni shirye-shirye suka kammala kuma jam’iyar zarayi taron da ba a taba irinsa ba.
Ya kuma ce an fitar da kwamitoci daban-daban guda goma sha tara (19) da zasu tabbatar da zaben ya kammala cikin nasara.
Rahotanni dai sun bayyana cewa har zuwa daren jiya Lahadi jagororin jam’iyar ta APC na tattaunawa don yin masalaha kan dantakara guda daya da zai yiwa jam’iyar takarar shugaban kasa sai dai ba akai ga cimma matsaya ba.