Daga Zara Jamil Isa
Dan takarar Gwamnan Jihar Kano a tutar jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf yace Idan al’ummar Jihar Kano suka zabe shi a zabe mai zuwa zai dawo da martabar Kano ta hanyar gudanar da aiyukan cigaba.
Abba Kabir Yusuf Wanda ake yiwa lakabi da Abba Gida-Gida ya bayyana hakan ne yayin da yake Jawabin godiya bayan tabbatar da shi a Matsayin Dan takarar Gwamnan Kano a jam’iyyar NNPP .
Yace mun tsara yadda zamu gabatar da aiyukan aiyukan Raya Kasa da cigaban al’umma Waɗanda suka hadar da bunkasa Ilimi,Noma samar da aiyukan yi ga Matasa ta hanyar bayar da jari ,Lafiya, inganta tsaro, baiwa Kananan Hukumomi dama, samar da hanyoyi da dai Sauransu.
Abba Kabir Yusuf ya Kuma Kalubalanci Gwamnatin Jihar kano bisa yadda ta yi watsi da muhimman aiyukan cigaba da gwamnatin Kwankwasiyya ta girgiro.
“Zamu yi gwamnati budadiya wacce zata tafi da kowa , Inda zamu Rika tuntubar masu Ruwa da tsaki a duk Inda buƙatar hakan ta taso” inji Abba Gida-Gida
Dan takarar ya yaba da yadda jam’iyyar NNPP take Samun karbuwa a Kano da duk jihohin kasar nan, Inda ya bayar da tabbacin Idan al’ummar Jihar Kano suka zabi jam’iyyar a 2023 zai gabatar da kyawawan manufofin jam’iyyar.